15 Maris 2022 - 20:15
Amir Abdullahiyan Yace: Fadada Dagantaka Tsakaninsu Da Rasha Yana Da Muhimmanci Sosai

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossain Amir-Abdollahiyan y aisa birnin Moko na kasar rasha domin tattaunawa game da muhimman batutuwa da suka shafi kasashe a mataki na kasa da kasa da kuma tattaunawar Vieanna . A lokacin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Rasha Sergie Lavrov , Abdallahiyan ya jinjinawa tawagar kasar rasha a tattaunawar Vieanna na ganin an cirewa iran Takunkumi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Idan ana biye da mu tun a shekara ta 2015 aka rattaba hannun kan yarjejniyar nukiliya tsakanin Iran da kasashen faransa jamus birtaniya rasha da kuma kasar China da ake kira da JCPOA amma Amurka ta kawo cikas bayan da fice ba bisa ka’ida ba a shekara ta 2018 tare kuma da kakabawa iran sabbin takunkumi

Haka zalika ministan ya fadi cewa ganawar ta su wata dama ce da zasu tattaunawa game da ci gaban da ake sama a kasashen Ukrani Afghanistan Yamen da kuma kasar Siriya .

Ana sa bangaren Sergei Lavrov ya fadi cewa ana gab da kawo karshen tattaunawar , kuma hulda kasuwanci tsakanin Iran da rasha idan aka kwatanta da shekarar bara ya karu da kashi 80 cikin dari .

342/